Showing posts with label LABARAN NAJERIYA. Show all posts
Showing posts with label LABARAN NAJERIYA. Show all posts

Thursday, December 14, 2017

Soja Ya Kashe Wani Bahaushe Mai Safarar Shanu Saboda Cin Hancin Naira 500


Wani jami'in sojan Nijeriya da aka bayyana sunansa a matsayin Sunday, ya kashe wani Bahaushe mai safarar shanu mai suna Shafi'u Garba saboda kin bada cin hancin naira dari biyar a daidai shingen bincike na sojoji a jihar Edo.

Lamarin ya auku ne a lokacin da marigayi Shafi'u, wanda aka fi sani da Ganda ya dauko shanu a mota daga garin Wudil dake jihar Kano zuwa jihar Edo.

Ganau ba jiyau ba, sun tabbatar da cewa lamarin ya auku ne a shingen bincike na sojoji dake Uromi a tsakanin Auchi da Benin da misalin karfe shida na yamma a ranar 8 ga Disamba, 2017.

Wani da lamarin auku a gaban sa mai suna, Sani Abdullahi, wanda suke cikin mota daya da marigayin, ya ce sojan ya harbi Garban ne a kai, inda bayan 'yan awanni ya mutu.

"Bayan mun wuce shingen sojojin ne sai kawai muka ga sojojin sun biyo sahun a mota, sai marigayi Shafi'u ya shawarce mu da mu tsaya"

“Bayan mun tsaya sai sojan ya shuna mana bindiga tare da harbi uku. Harsashi na farko ya samu rufin motar ne, yayin da kuma harsashi na biyu ya samu Shafi'u a kai".

Malam Sani ya kara da cewa babu wanda ya tsayar da su a yayin da suka iso shingen binciken. Amma bayan sun wuce sai sojojin suka biyo su a mota suna cewa me ya sa suka wuce ba tare da sun ajiye naira biyar kafin sun wuce shingen ba.

Buhari Zai Kafa Wata Dirkekiyar Tashar Makamashin Gas A Arewa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Da alamar yankin arewacin Najeriya ya yi kusa ya rabu da matsalar rashin wutar lantarki da makamashi da rashin ayyukan yi da kuma durkushewar kamfanoni da tabarbarewar tattalin arziki.Wannan ko ya biyo bayan matakin da Shugaba Buhari ya dauka na kafa wata tashar makamashin gas wadda bututanta za su wanzu zuwa sassa dabandaban.
Nan ba da dadewa ba ‘yan kasashen waje irinsu China da sauransu za su rika ribibin zuwa arewacin Najeriya kafa jari saboda za a kafa wata makekiyar tashar makamashin gas a Ajakuta, inda za a shinfida bututai daga Ajakutan zuwa sassan arewacin Najeriya musamman ma Abuja da Kaduna da Kano. Sannu a hankali bututan za su isa wurare da dama na arewacin kasar.
Wannan tashar, wadda kafa ta zai ci dalar Amurka Miliyan dubu dari biyu ($200,000m) za ta magance matsalar rashin wutar lantarki a arewacin kasar ta yadda kamfanoni za su yi ta habaka. Yawan kamfanonin ciki da wajen Najeriya zai janyo ayyukan yi ga ‘yan arewacin Najeriya tare kuma da bunkasa tattalin arzikin yankin.
Kakakin Fadar Shugaban Najeriya Garba Shehu ya ce manyan kamfanoni su ma za su saka jari ciki ta yadda za a gudanar da tashar makamashin ba tare da cikakkiyar sa hannun gwamnati ba saboda a kula da tashar. Ya bayyana cewa muddun mutane su ka saka jari ciki to ba za su yadda a barnata wurin ba, Ya kwatanta irin kamfanonin da za a kafa sanadiyyar kafa tashar da irin kamfanonin da aka kafa a kuduncin Najeriya da kuma wasu kasashen Afirka, inda kasashe irin China da Turai ke ta saka jari saboda yalwar makamashin gudanar da manyan kamfanoni.

Monday, December 11, 2017

An Sako Shugaban Jam'iyyar PDP Na Jihar Filato Damishi Sango

A makon da ya shige ne, wasu da ba'a tantance ba suka sace shugaban jam'iyyar PDPna reshen jihar Filato da wasu mutane hudu da suke tare dashi a kusa da Jere cikin ihar Kaduna akan hanyarsu ta zuwa Abuja
Wadanda suka sace shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Filato kuma tsohon ministan wasannin Nigeriya, sun sakoshi tare da mutane hudun da suka yi garkuwa dasu.
A karshen makon da ya shige ne, da yamma, aka sace shugaban tare da wani kusa a jam'iyyar Emmanuel Mannil da wasu mutane uku a yankin Jere cikin jihar Kaduna a kan hanyarsu ta zuwa Abuja wajen taron kasa na jam'iyyarsu da aka kammala jiya Lahadi.
Kakakin jam'iyyar a Filato Mr. John Akans ya tabbatar da sako shugaban da mutane hudun dake tare dashi. A cewarsa suna cikin koshin lafiya. Ya yiwa Allah godiya tare da wadanda suka taimaka aka sakosu.
Inji Mr. Akans Allah ne kadai ya kiyayesu domin jikin motar da suke ciki yayinda aka sacesu duk an yi mata raga-raga da harsashi. Ya ce yana gida yana hutawa daga azabar da suka sha.
Wadanda suka yi garkuwa dasu sun ce yunwar da gwamnatin yanzu ta jefasu ciki ta sa suke sace mutane. Wai ba sonsu ba ne. Injishi an tilasta wa shi Sango ya yi tafiyar awa 24. Da aka sakosu da dare an basu tocilan sun kuma yi tafiyar awa 22. Bugu da kari sun yi kwana uku babu ci ko sha.
Dangane da kudin fansa na kusan Nera miliyan dari da barayin suka nema a basu, Mr. Akans ya ce shi bashi da bayanin da zai bayar. Sai sun samu cikakken bayani tukunna.

Thursday, December 7, 2017

MARYAM SANDA TA KARA BAYYANA A GABAN KOTU

 An ci gaba da sauraron karar Maryam Sanda akan zargin da ake mata na kisan mijin ta Bilyaminu. A zaman shari'ar na ranar Alhamis, Maryam ta tsaya a gaban mai shari'ar rike da carbi a hannunta. Sai dai alkalin ya dakatar da ci gaba da shari'ar saboda a cewarsa, sai 'yan sanda sun kawo wasu mutum uku da ake zargi da jirkita hujjojin da za su iya taimakawa wajen gano yadda aka kashe Bilyaminu.

Wadannan mutum ukun sun hada da wata Maimuna Aliyu da Safiya Aliyu, wadanda ake kyautata zaton makusantan Maryam ne.
Sai dai 'yan sandan sun ce ba su samu damar aikewa da mutanen sammaci ba ne, shi ya sa ba su gurfana a gaban kotun ba.

Amma alkalin ya ce bai ga wata alama da ke nuna cewa 'yan sandan sun yi iya kokarinsu da ke nuna cewar sun aike wa da mutanen sammaci ba. Masu shigar da karar dai sun yi alkawarin cewa za su kawo mutane ukun da ake zargi da jirkita hujjojin ranar 14 ga watan Disamba, inda za a ci gaba da sauraron karar.

A wannan karon dai wani sanannen lauya mai suna JB Dawudo ne yake kare Maryam a shari'ar, kuma ya nemi alkali ya bayar da belinta zuwa ranar da za a sake zaman kotun. Sai dai alkalin kotun Yusuf Halilu, ya yi watsi da bukatar lauyan, inda ya ki bayar da belinta, amma ya ba shi damar ganawa da ita na tsawon minti 20 kafin a wuce da ita gidan yarin Suleja.

An Yankewa Wani Matashi Hukuncin Rataya

An yankewa Wani mutum mai suna John Yakubu hukuncin kisa ta rataya akan laifin yankan rago da yayi wa wani yaro mai shekaru bakwai mai suna Samuel Danjuma a shekarar 2012, a jihar Nasarawa.
Mai shari’a James Abundaga na kotun jihar Nassarawa ne ya yanke hukuncin inda aka samu wanda ake zargi da laifin aikata hakan a yau laraba. Yace hukuncin yayi daida da sashi na 221 na kudin tsarin shari’ar jihar inda wanda ake zargin ya fallasa kanshi.
Jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin ne tare da wani Ishaya Daklung ranar 22 ga watan Yulin shekarar 2012. Mai shari’an ya ce an kama Yakubu ne da kan yaron a kunshe a leda kana ya fada musu yadda akayi yayi wa yaron wayo ya ja shi zuwa rafin Agwan Galadima dake karamar hukumar Nassarawa inda anan ne ya nutsar da shi cikin ruwa bayan haka kuma ya yanka shi.
Mai shari’a Abundaga ya yankewa dayan wanda ake zargin wato Dalung, hukuncin shekaru 4 a gidan yari da aiki mai tsanani wanda yace hukuncin yayi daidai da sashi 219 na tsarin doka.

Tuesday, December 5, 2017

Za a Yi Wa 'Yan Sandan SARS Garambawul a Najeriya

Biyo bayan korafe-korafe akan sashen 'yan sandan Najeriya dake yaki da masu fashi da makami akan zalunci da suke yi wa mutane da rashin kwatanta adalci da gaskiya ne ya sa babban sifeton 'yan sandan Najeriya bada umurnin yi wa sashen gyaran fuska.
Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya ba da umurnin yin garambawul ga sashen rundunar dake yaki da 'yan fashi da makami, wato SARS.
A cewar babban sifeton yanzu kwamishanan 'yan sanda ne daga hedkwatar rundunar dake Abuja zai zama jagoran sashen ba daga matakin jihohi ba kamar yadda aka saba.
Baya ga yin sauyin a sashen shugabanci, za a kuma horas da 'yan sashen sanin hakkin bil adam domin su daina cin zarafin jama'a ba tare da ikon shari'a ba.
Kafin sanar da wannan matakin da babban sifeton ya dauka, 'yan Najeriya sun yi koka kan sashen tare da kiran mahukuntan kasar da su soke sashen sabili da tsanananin rashin imaninsu. Baya ga musgunawa mutane ba gaira ba dalili, ana kuma zargin sashen da tatsar mutane kudade sai su jefa a aljuhunsu maimakon su ba gwamnatin Najeriya.
Sashen ya yi kaurin suna domin ko a shirin Muryar Amurka na 'Ciki da Gaskiya,' an kawo labarin wasu Fulani makiyaya daga jihar Kogi dake korafin 'yan sandan na SARS sun damke masu 'yan uwa har na tsawon wata takwas ba shari'a.
Daya daga cikin Fulanin Jihar Kogin, Yusuf Bature ya yi karin haske inda ya kira gwamnatin Buhari ta yi binciken tsakani da Allah a kuma hukunta duk wanda ya yi laifi. Amma ba zasu yarda da dauke masu dukiyoyi tare da yawo da hankulansu wata da watanni domin wai ana ganin su Fulani basu da ilimin boko. Ya kara da cewa, ya kamata Shugaba Muhammad Buhari ya ji maganar saboda akwai wadanda suke aiki a gwamnatinsa da suke kokarin bata masa aiki.
Kungiyar Amnesty International ita ma ta yi fatan samun adalci ga wadanda ake cin zarafinsu ba tare da sahihiyar hujja ba. A cewar wani dan kungiyar,
"Duk mutumin da yake da matsala ta take hakkin bil Adama, babbar bukatarsa ita ce a yi masa adalci.Wasu 'yan uwansu aka kashe babu gaira babu dalili maimakon a hukunta masu laifin sai magana ta zama tamkar wasan yara."

Monday, December 4, 2017

An Kammala Taron Kasa da Kasa Akan Ta'addanci a Kasar Jordan

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari na cikin shugabannin da suka kasance a taron kasa da kasa da ya gudana a Jordan akan musabbabin dake haddasa ta'addanci da wasu miyagun dabi'u da yadda za'a yakesu

Yayinda ya kasance a taron, shugaban Najeriya Muhammad Buhari, ya ce babu shakka miyagun kalamu da miyagun wa'azi da wasu malamai su keyi na gaba gaba wajen haddasa ta'addanci a nahiyar Afirka da ma duniya gaba daya.
A ganin shugaba Buhari wajibi ne a yi tsarin da zai tabbatar cewa malaman addini sun yi wa'azi na gaskiya da adalci domin kawar da tashe tshen hankula.
Ministan tsaron Najeriya Manjo Janar Mansu Dan Ali, wanda yake cikin tawagar shugaba Buhari, ya ce akwai wasu muhimman abubuwa da yakamata a yi domin a nuna cewa ta'addanci ba abu ba ne nagari. Ya yi misali da maganar wa'azi da juya tunanen mutane su zama masu tsatsauran ra'ayin addini, duk wadannan ya kamata a san yadda za'a dakilesu domin a samu kwanciyar hankali.
Akan abubuwan dake faruwa a cikin Najeriya da suka haddasa rikici ko zasu iya haddasa wasu kamar kashe shugaban Boko Haram na farko, Muhammad Yusuf tare da ci gaba da tsare shugaban kungiyar Shiya, wato Shaikh Ibrahim El-zakzaki, Janar Mansur Dan Ali ya ce suna cikin abubuwan da aka gano. Suna cikin rashin adalci da rashin gwamnati ta kwarai.
A taron an bukaci shugabannin su dinga yiwa mutanesu adalci kuma a Najeriya an kama hanyar yin hakan.
Dangane da maganar Yusuf Muhammad Janar Mansur ya ce har yanzu maganar tana gaban shari'a a kotu saboda haka ba zai iya ce komi a kai ba. Sai a bari sai an kai karshen shari'ar.

An Sake Samun Barkewar Rikici a Jihar Adamawa

Tun makon jiya aka shiga wani rikici tsakanin 'yan kabilar Bachama dake yankin Numan da makiyaya inda har aka samu asarar rayuka sai kuma gashi wani rikicin ya sake barkewa a yankin dake cikin jihar Adamawa

Wani jami'in 'yan sandan jihar Adamawa ya yiwa wakilin Muryar Amurka dake Yola, Ibrahim Abdulaziz, bayanin abubuwan dake faruwa.
Dangane da matakan da suka dauka a matsayinsu na jami'an tsaro ya ce sun baza mutanensu a duka kauyukan da aka kai hari da kewayensu. Ya tabbatar da samun labarin barkewar rikici a kauyen Dung dake cikin karamar hukumar Demsa. Ya ce hankulan sojojin sama da na kasa da 'yan sanda sun koma yankin. Injishi sun dauki duk matakan tsaron da suka kamata su dauka. Ya kara da kiran jama'a da su daina yin aiki da jita jita saboda wai sun samu wasu rahotanni amma da suka duba lamarin sai ya kasance sabanin abun da aka gaya masu.
A kan ko rayuka nawa suka salwanta jami'in tsaron ya ce bashi da labari. Sai dai ya yi alkawarin bada duk wani karin bayani da suka samu nan gaba.
Dangane da labarin cewa an tare hanyar zuwa Gombe daga Yola ana tsayar da motoci ana kashe mutane, jami'in ya karyata batun. Ya ce babu gaskiya ciki saboda motocinsu suna sintiri akan hanyar. Bugu da kari, sun kara jami'an tsaro a hanyar. Suna kuma jaddadawa jami'ansu su tabbatar ba'a samu irin wannan lamarin ba a hanyar.
Akan Savana tare da cewa an kona kamfanin Savana, har wa yau jami'in ya ce duk jita jita ne saboda akwai jami'ansu da yawa a yankin Savanan.

Friday, October 6, 2017

Malaman Makaranta Fiye da 500 Aka Kashe Sanadiyar Rikicin Boko Haram a Jihar Borno

Kungiyar Malaman Makaranta ta jihar Borno a bikin ranar malamai da aka yi a Borno



Yayin bikin ranar malaman makaranta ta duniya da aka yi a jihar Borno gwamnatin jihar ta sanar cewa tayi hasarar malamanta fiye da dari biyar a shekaru shidan da aka yi ana fama da rikicin Boko Haram
Yayinda ake bikin “Ranar Malaman Makaranta ta Duniya” jiya 5 ga watan Oktoba, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ta kowace shekara don tunawa da karrama malamai, gwamnatin jihar Borno a Nigeria tayi kira akan kungiyoyi masu zaman kansu da su ci gaba da dafawa harkokin ilimi a jihar da yanzu haka ke tangarari sakamakon illar da Boko Haram ta yiwa sha’anin ilimi a jihar, abinda ya janyo mutuwar malamai fiye da 500 da aka kashe.
A cewar mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Usman Durkwa, gwamnatin jihar ta dukufa wajen inganta harkokin ilimin zamani a jihar tare da biyan bukatun malamanta duk da matsalolin da jihar ke fuskanta.
Alhaji Durkwa ya tunashe da jama’a irin matsalolin da kungiyar Boko Haram ta haifarwa jihar ta fannin ilimi inda har ya kusa durkushewa baki daya. Sai dai yace gwamnatin jihar ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen inganta ilimi.
Gwamnatin jihar ta dukufa wajen gyaran duk makarantun jihar da suka lalace musamman wadanda aka sake kwatowa daga hannun ‘yan Boko Haram a wuraren da suka mamaye a da can.
Shi ma kwamishanan ilimin jihar, Musa Inuwa Kufo ya sanar cewa gwamnan jihar, Kashim Shettima, ya saki kudin biyan hukumomin jarabawar kare karatun sakandare irinsu WAEC da NECO domin a sakowa daliban da suka kammala karatunsu sakamakon jarabawar da suka dauka.
Shugaban kungiyar Malaman jihar ya bayyana farin cikinsu tare da kuma abubuwan da suke ci masu tuwo a kwarya, inda ya bada misali da rashin biyansu kudin karin girma da na alawus alawus da kuma samar musu ingantattun kayan aiki.