Thursday, December 7, 2017

MARYAM SANDA TA KARA BAYYANA A GABAN KOTU

 An ci gaba da sauraron karar Maryam Sanda akan zargin da ake mata na kisan mijin ta Bilyaminu. A zaman shari'ar na ranar Alhamis, Maryam ta tsaya a gaban mai shari'ar rike da carbi a hannunta. Sai dai alkalin ya dakatar da ci gaba da shari'ar saboda a cewarsa, sai 'yan sanda sun kawo wasu mutum uku da ake zargi da jirkita hujjojin da za su iya taimakawa wajen gano yadda aka kashe Bilyaminu.

Wadannan mutum ukun sun hada da wata Maimuna Aliyu da Safiya Aliyu, wadanda ake kyautata zaton makusantan Maryam ne.
Sai dai 'yan sandan sun ce ba su samu damar aikewa da mutanen sammaci ba ne, shi ya sa ba su gurfana a gaban kotun ba.

Amma alkalin ya ce bai ga wata alama da ke nuna cewa 'yan sandan sun yi iya kokarinsu da ke nuna cewar sun aike wa da mutanen sammaci ba. Masu shigar da karar dai sun yi alkawarin cewa za su kawo mutane ukun da ake zargi da jirkita hujjojin ranar 14 ga watan Disamba, inda za a ci gaba da sauraron karar.

A wannan karon dai wani sanannen lauya mai suna JB Dawudo ne yake kare Maryam a shari'ar, kuma ya nemi alkali ya bayar da belinta zuwa ranar da za a sake zaman kotun. Sai dai alkalin kotun Yusuf Halilu, ya yi watsi da bukatar lauyan, inda ya ki bayar da belinta, amma ya ba shi damar ganawa da ita na tsawon minti 20 kafin a wuce da ita gidan yarin Suleja.

0 comments:

Post a Comment