Tuesday, January 3, 2017

Nigeria: Shirin tallafin 5,000 duk wata ga talakawa ya fara aiki

Gwamnatin Najeriya ta ce ta fara bayar da tallafin Naira 5,000 ga matalauta miliyan daya a sassan kasar daban daban.
Shirin wanda aka fara a jihohi tara, wani bangare ne na yunkurin tallafawa marasa galihu da Shugaba Muhammadu Buhari da jami'aiiyar APC suka yi a lokacin yakin neman zabe.
Wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ya fitar ta ce an biya kudin ne ta wani tsari na musamman da gwamnatin tarayya ta kirkiro dan tallafawa mabukata.
Sanarwar ta ce 'yan Najeriya miliyan daya ne za su ci gajiyar shirin, inda za su din ga karbar tallafin a kowanne wata, kamar yadda ya ke a cikin kasafin kudin bara.
Mista Akande ya ce tuni wasu daga cikin 'yan kasar suka tabbatar da fara karbar tallafin kudin tun a makon da ya wuce, a lokacin da shirin ya fara aiki.
''Rukunin farko sun karbi kudaden a jihohin kasar nan tara a ranar Juma'ar karshe ta watan Disamba, kuma nan da ba da jimawa ba za a bai wa sauran jihohi biyar na su kudin dan cike gurbin rukunin farko na shirin'', in ji shi.
Jihohin da suka fara karbar tallafin sun hada da jihar Borno, Kwara, Cross Rivers, Niger, Kogi, Oyo, Ogun da kuma Ekiti.
Sai dai wasu masu sharhi na ganin zai yi wuya a iya tantance mabukatan ganin cewa babu wani cikakken kundin ajiye bayanai a kasar.
Amma Mista Akande ya ce an fara da wadannan jihohi ne saboda gwamnatocinsu na da kididdigar mutanen da ba su da karfi da ya kamata su samu tallafin.

0 comments:

Post a Comment