Tuesday, December 5, 2017

Za a Yi Wa 'Yan Sandan SARS Garambawul a Najeriya

Biyo bayan korafe-korafe akan sashen 'yan sandan Najeriya dake yaki da masu fashi da makami akan zalunci da suke yi wa mutane da rashin kwatanta adalci da gaskiya ne ya sa babban sifeton 'yan sandan Najeriya bada umurnin yi wa sashen gyaran fuska.
Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya ba da umurnin yin garambawul ga sashen rundunar dake yaki da 'yan fashi da makami, wato SARS.
A cewar babban sifeton yanzu kwamishanan 'yan sanda ne daga hedkwatar rundunar dake Abuja zai zama jagoran sashen ba daga matakin jihohi ba kamar yadda aka saba.
Baya ga yin sauyin a sashen shugabanci, za a kuma horas da 'yan sashen sanin hakkin bil adam domin su daina cin zarafin jama'a ba tare da ikon shari'a ba.
Kafin sanar da wannan matakin da babban sifeton ya dauka, 'yan Najeriya sun yi koka kan sashen tare da kiran mahukuntan kasar da su soke sashen sabili da tsanananin rashin imaninsu. Baya ga musgunawa mutane ba gaira ba dalili, ana kuma zargin sashen da tatsar mutane kudade sai su jefa a aljuhunsu maimakon su ba gwamnatin Najeriya.
Sashen ya yi kaurin suna domin ko a shirin Muryar Amurka na 'Ciki da Gaskiya,' an kawo labarin wasu Fulani makiyaya daga jihar Kogi dake korafin 'yan sandan na SARS sun damke masu 'yan uwa har na tsawon wata takwas ba shari'a.
Daya daga cikin Fulanin Jihar Kogin, Yusuf Bature ya yi karin haske inda ya kira gwamnatin Buhari ta yi binciken tsakani da Allah a kuma hukunta duk wanda ya yi laifi. Amma ba zasu yarda da dauke masu dukiyoyi tare da yawo da hankulansu wata da watanni domin wai ana ganin su Fulani basu da ilimin boko. Ya kara da cewa, ya kamata Shugaba Muhammad Buhari ya ji maganar saboda akwai wadanda suke aiki a gwamnatinsa da suke kokarin bata masa aiki.
Kungiyar Amnesty International ita ma ta yi fatan samun adalci ga wadanda ake cin zarafinsu ba tare da sahihiyar hujja ba. A cewar wani dan kungiyar,
"Duk mutumin da yake da matsala ta take hakkin bil Adama, babbar bukatarsa ita ce a yi masa adalci.Wasu 'yan uwansu aka kashe babu gaira babu dalili maimakon a hukunta masu laifin sai magana ta zama tamkar wasan yara."

0 comments:

Post a Comment