Thursday, December 14, 2017

Soja Ya Kashe Wani Bahaushe Mai Safarar Shanu Saboda Cin Hancin Naira 500


Wani jami'in sojan Nijeriya da aka bayyana sunansa a matsayin Sunday, ya kashe wani Bahaushe mai safarar shanu mai suna Shafi'u Garba saboda kin bada cin hancin naira dari biyar a daidai shingen bincike na sojoji a jihar Edo.

Lamarin ya auku ne a lokacin da marigayi Shafi'u, wanda aka fi sani da Ganda ya dauko shanu a mota daga garin Wudil dake jihar Kano zuwa jihar Edo.

Ganau ba jiyau ba, sun tabbatar da cewa lamarin ya auku ne a shingen bincike na sojoji dake Uromi a tsakanin Auchi da Benin da misalin karfe shida na yamma a ranar 8 ga Disamba, 2017.

Wani da lamarin auku a gaban sa mai suna, Sani Abdullahi, wanda suke cikin mota daya da marigayin, ya ce sojan ya harbi Garban ne a kai, inda bayan 'yan awanni ya mutu.

"Bayan mun wuce shingen sojojin ne sai kawai muka ga sojojin sun biyo sahun a mota, sai marigayi Shafi'u ya shawarce mu da mu tsaya"

“Bayan mun tsaya sai sojan ya shuna mana bindiga tare da harbi uku. Harsashi na farko ya samu rufin motar ne, yayin da kuma harsashi na biyu ya samu Shafi'u a kai".

Malam Sani ya kara da cewa babu wanda ya tsayar da su a yayin da suka iso shingen binciken. Amma bayan sun wuce sai sojojin suka biyo su a mota suna cewa me ya sa suka wuce ba tare da sun ajiye naira biyar kafin sun wuce shingen ba.

0 comments:

Post a Comment