Thursday, May 25, 2017

SHIGOWAR WATAN AZUMI GUZURI MAFI ALBARKA GA 'YAN KASUWA.

SHIGOWAR WATAN AZUMI GUZURI MAFI ALBARKA GA 'YAN KASUWA.


PRESENTIONLOAD__

Azumi a addinin Musulunci na nufin kauracewa cin abinci, shan ruwa, fadin munanan maganganu, shan taba, saduwa tsakanin ma'aurata da kuma dukkan wani aiki da ya sabawa koyarwa addinin Musulunci tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana da nufi bautawa Allah madaukakin sarki, Azumi na daya daga cikin shika-shigan Musulunci guda biyar, haka tasa ya zama wajibi ga dukkan Musulmin da ya balaga, a duk watan tara Ramadan na shekarar Musulunci, A watan Ramadan Allah ya saukar da Al-Qur'ani mai tsarki ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Watan azumi wata ne na rahma, alfarma, gafara da karbar addu'a. Wata ne da dukkan wani Musulmi ke kara dagewa wurin ibada da kyautatawa 'yan uwa Musulmai don samun rahmar Allah.

Kuma akwai da yawan 'yan kasuwa a fadin kasar nan sai kaga tamkar jira suke yi a ce watan azumi ya kama lokaci guda kamar da hadin baki sai su tashi kaya, hakan yakan jefa talakawa cikin ha'ula'i bayan akwai wadanda koda kayan da sauki ma basa samu su sayi kayan ta dadin rai ballantana kuma a ce an karawa kayan masarufi farashi. Duba da yadda a baya 'yan kasuwa ke kuka da Dala to yau ga shi tayi sakko amma abin mamaki wasu daga cikin Musulmai na yin amfani da wannan wata mai albarka wajen kara tsauwalawa 'yan uwa Musulmai, misali wasu daga cikin 'yan kasuwa da zarar watan azumin ya kusanto sai su fara tashin farashin kayan masarufi kamar shinkafa, nama, lemo, dankalin turawa, kwai,.kayan miya da sauran kayan masba ufi saboda ganin ya zama wajibi ayi amfani dasu, saboda duk wanda ya sha ruwa zaiso yadan karya da abinci mai dadi cikin kayan da ake shigowa da shi muddin idan ku ka kii rage farashi kamar yadda Dala ta fadi, to lallai za mu gaskata gwamnati cewa ku kuke karawa kaya farashi da gangan.

'Yan kasuwa gaskiya ya kamata kuji tsoron Allah musamman da akwai kayayyakin da suke lalatattu wasu sun tashi daga aiki amman sai ake amfani da shi ta hanyar canja musu kwalaye mutane kuma su yi amfani da shi har ya zama anyi amai da gudawa, duk fa a na yin wannan ne akan neman kudi kuma wannan ba shi ne zai tseratar da mutane ba rayuwar kanta 'yar kalilan ce ga abin ta kaici shi ne Ribage a fito da shinkafa ko dai wani abu sai a bude bakin buhu a zazzagi kwano daya ko rabi wannan duk haramun ne ko kuma a zuba shikafar gida a cikin buhun shinkafa 'yar kasar waje duk wannan bai dace ba a na batawa 'yan kasuwa na gari suna duk lalacewar duniya ba'a rasa na Allah.

Shin bama ganin yadda 'yan kasuwa mabiya addinin Kirista ke yi ne da zarar an ce lokacin Kirismeti yazo zasu rinka rage farashin kayayyaki saboda masu raunin cikin su su samu damar yase, bai kamata a ce su suke wannan aikin kyautatawa ba mu ba, Kuma yana da kyau mu kammu sauran al'umma mu gyara halayan mu tsakani da Allah mu tuba kyakykyawan tuba tu daga kan ma'aikatan gwamnati, 'yan kasuwa, 'yan dako da lebura, wallahi irin wannan halin da muke ciki muma akwai halayan mu, dan uwa karfa kace zaka ga laifin wani A'a fara duba naka tundaga cikin gidan ka cikin zamantakewar ka da al'umma tare da ta iyalan ka, mawadata a taimakawa marasa hali musamman makofta da wanda suke cikin mu.

A cikin wannan wata mai albarka da muka shigo Allah Ta'ala ya karbi ibadunmu, Allah yasa muna cikin wadanda za'a yanta a yi musu gafara, Allah ya taimaki yankin mu Allah ya bawa shugaban kasar Muhammadu Buhari lafiya Allah ya kara hada kawunan shugabannin mu a jihar kano dama kasa baki daya, Allah ya hane mu da aikin da na sani a rayuwar mu, Allah yasa mu ciki da imani, Amin.

0 comments:

Post a Comment