Thursday, May 25, 2017

Batun Harbe Masu Yunkurin Juyin Mulki A Najeriya.

RA'AYI RIGA:


Kowa Da Irin Ta-sa__Batun Harbe Masu Yunkurin Juyin Mulki A Najeriya.



PRESENTIONLOAD__
A makwan da ya gabata ne aka yi yunkurin shirya juyin mulki a Najeriya, wanda bai yi nasara ba, dalilin da ya jawo wasu daga cikin manyan kasashe duniya, irin su Birtaniya, suka ja kunnen sojojin Najeriya, tare da yin Allah wadai da batun.


Hakan ya sa babban hafsan sojin kasar, Gen-Tukur Yusuf Buratai, shan alwashin harbe duk mutumin da ya samu da hannu a yunkurin juyin mulkin.


Shin menene ra'ayoyinku dangane da wannan batu, shin da ace wannan yunkuri na juyin mulki, ya yi nasara, wane mataki yan Najeriya, za su dauka.


Kuma ya dace Gen-Buratai, din ya harbe duk wanda ya samu da hannu a yunkurin, kuna goyon bayan hakan__Bayyana ra'ayinka yanzu.

0 comments:

Post a Comment