Friday, December 30, 2016

Babu adalci a kalaman Kerry - Natanyahu

Farayin Ministan Isra'ila Benjamin Natanyahu ya yi tir da kalaman da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi kan matsalar kasarsa da Falasdinawa a zaman na goyon bayan bangare daya.
A ranar Laraba ne Mr. Kerry ya furta cewa shirin kirkiro kasashe biyu na Isra'ila da Falasdinu a zaman wata hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya na cikin hadari kuma gina matsugunan yahudawa a yankunan Falasdinawa babbar matsala ce.
A cikin wani jawabi da aka watsa kai tsaye ta gidan tallabiji, Mr. Natanyahu ya ce kalaman na John Kerry babban abin bacin rai ne kuma ba bu adilci ciki.
Ya kara da cewa ai musabbabin rikicin shi ne kin amincewa da kafuwar kasar Isra'ila da Falasdinawa suka yi, amma Mr. Kerry bai dubi wannan ba.
Karin martani
Bayan kalaman na John Kerry, Donald Trump ya rubuta a shafinsa na Twittter cewa yana goyon bayan Isra'ila kuma ba zai bari a yi ma ta cin-mutunci ba.
Ya bukaci Isra'ila da kada ta karaya, har ya karbi mulki a watan gobe.
Shi kuwa Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, da yake mayar martani kan kalaman Mr. Kerry, ya ce a shirye yake ya sake komawa kan teburin shawara da Isra'ila.
Shugabannin Falasdinawa dai na goyon bayan wani taron kasa-da-kasa kan zaman lafiya da za a yi a birnin Paris wata mai zuwa - duk da adawar da Isra'ila ke yi da hakan- kuma sun ce suna aiki kut-da-kut da kasar Faransa domin samun nasarar taron.

0 comments:

Post a Comment