Wednesday, December 28, 2016

Ba mu amince da dokar daidaiton rabon gado ba - Sultan

Mai alfarma sarkin Musulmi ya yi watsi da kudurin dokar da za ta kawo daidaito tsakanin mace da namiji wajen rabon gado a Najeriya.
Muhammad Sa'ad Abubakar yace ba za a amince da duk wata doka da za ta yi wa dokokin addinin musulunci karan tsaye ba, inda maza su ke daukar kaso mafi rinjaye akan mata idan aka zo batun rabon gado.
A watan Oktoba ne, kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta amince da kudurin dokar, wadda masu fafutuka suka ce za ta taimaka wajen rage nunawa mata banbanci.
A watan Maris, 'yan majalisa sun yi watsi da kudurin dokar, suna cewa ba ta dace da addini da kuma al'adun wasu 'yan Najeriya ba.
Da ya ke magana a wurin gasar karatun al-Kur'ani a garin Zamfara, Sultan ya ce: "Addininmu shi ne hanyar rayuwarmu. A don haka ba za mu amince da duk wani yunkuri na sauya abin da Allah ya halatta mana ba."
Ya kara da cewa: "Musulunci addinin zaman lafiya ne; mun dade muna zaune lafiya da Kiristoci da mabiya sauran addinai.
A don haka ya kamata a bar mu mu yi addininmu yadda ya kamata".
'Yan majalisar sun ce za a yi zaman jin ra'ayin jama'a tukunna kafin su dauki matsaya kan kudurin.

0 comments:

Post a Comment