Wednesday, January 13, 2021

AUREN FANSA 1&2





 Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin

mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi, wanda
zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka,
don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma
tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka
fuskarta ta kanyi ja.
A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga
bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma matar
tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa
cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye
6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali har
yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke kwance
tana kukan fitar rai.
A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin
wata irin sigar rarrashi.
"Hajiya Bilki."
Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da
takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata.
A hankali ya soma magana.
"Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar
kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah
ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki
wallahi."
Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma
zuciyarsa ta raunana!
Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta
tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye
bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana
cikin 6acin rai.
"Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain
nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya
za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure
amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa
ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke
gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin
ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan
gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni
ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata
mujiya haba!"
Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse
idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa,
tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma
yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin
haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin
kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana.
"Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba
Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai
hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce
sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka zaiyi
dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole sai
kin samu haihuwa
zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya
baki kyau, arzik'i ya wadata ki
da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har
akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?"
Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa
da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya
cigaba da magana.
"Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki
idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai
baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata
yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa
sannan ki rok'e sa gafara da rahama.
Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba
tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi.
Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o,
kina jina?"
Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta
ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na
manya yace.
"Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa
nakeji."
Ta6e baki tayi tace
"Kayi hak'uri na manta ban girka ba."
Yayi murmushi yace
"Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe
amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare shi?"
Tace
"Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya
kamata ka barni na huta mana."
Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake
Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi
murmushi yace
"Haka ne Allah ya baki lafiya."
"Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta
gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga
d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki.
D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana fitowa
ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi kitchen,
fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo parlor
ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon tashar
Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas sannan
ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu a lokaci
guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka har bacci
ya sace sa.
Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da
ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm,
zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah,
bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin
Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya,
kiranta yayi a hankali.
"Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi
k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace
"Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana
fusakarsa ba annuri ko kad'an.
"Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har
lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi
sallah?"
Tace
"Kayi hak'uri na manta ne."
Girgiza kansa yayi yace
"Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na
gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo."
Ko kallonsa batayi ba tace
"To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama
mana."
Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya
shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar
nauyi ya fice daga gidan.
Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce gidan
Goggo dake cikin Layout a garin Katsina, yana
shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya saba
bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon
masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi
ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar
kullum sannan ta soko masa zancen da kullum
baya son shi.
"Ya maganar aure Hamza?"
Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana
son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin
hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa
dai na k'asa.
"Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma
ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana
buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar, idan
kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan kuma
bakada shi babu damuwa."
Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma
mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin
Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole
yace.
"Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan
zan zo na sanar dake."
Murmushi tayi tace
"Allah ya nuna mana."
Yace "Amin."
Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare,
gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce
d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito
parlor.
Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani
American series, jin alamun shigowa yasa ta
kalleshi lokaci guda kuma tace
"Har ka dawo?"
Yace
"Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera
yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa tayi
kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa.
Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse
shirun nasu
"Hamza, wai ya maganar mu ne?"
Yace
"Wace magana kenan?"
Ta zum6uro baki tace
"Ba dai har ka manta ba?"
Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce
tana son kud'i.
Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da
shagwa6a tace
"Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro
kaya."
Shiruyayi gami da sauke nannauyan numfashi
yace
"Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun
rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai
kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma
bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa
basai ki bata ba ta kawo maki."
Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi
don haka sai tace
"Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in
nawa zaka bani?"
Yace
"Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai
na k'ara maki."
Da sauri ta tashi zaune
"Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an."
A fusace ya tashi tsaye yace
"Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana,
ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki."
Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi
kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan
don ya fusata.
Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya
tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa
tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci.
K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman baya
jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a hanzarce
yake komai tashinta yayi daga bacci ya ce mata
zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace masa "Toh"
sannan ta ja bargo ta rufe har kanta. Girgiza
kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi.
Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai
lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office
d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko yaji
yunwa sai yaci kawai.
A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa kamar
kullum. Haka ya wuni yana juya maganar Goggo a
ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake sukuku
dashi har lokacin sallah sannan ya tashi ya fice
tare da sauran abokanan aikinsa musulmai.
Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro
gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa
data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin.
Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa
taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai
k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana
mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a
hankali ya ture ta yace
"Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa
kafin lokacin sallah yayi."
Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor
ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige d'akinsa.
Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen
don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da
cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan
dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a
kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da
kwarkwasa. Can kuma tace
"Alhaji."
Bai kalle ta ba yace
"Na'am."
Tace
"Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta shine
nake so ka bani kud'i na bata guddumawa ta..."
Da sauri yace
"Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da zancen
wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai ko?"
Murmushi tayi tace
"Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka
huta sai muyi magana."
Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita don
yaga lokacin sallar magriba ta gabato.
***
"Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya
rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata irin
makekiyar kujera tana duba magazine da glass
d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga ido ta
kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya haye bisa
cinyar ta yana mai hugging d'inta. Itama hugging
d'insa tayi tana kallonsa cike da so tace.
"Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?"
Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin
murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum
dogo fari ya shigo yana sanye da kayan hausawa
harda babbar riga, sai da yazo daidai bakin k'ofar
da zata sadasa da parlon yaja ya tsaya yana
murmushi, sannan kuma yace.
"Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya
lashe baki gaba d'aya wato overall as always."
Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake
tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana murmushi.
Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk
sosai a jikinta tace
"That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara maka
basira, toh saura na Islamiyya, idan har kayi
k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar maka
ta mussaman."
Cike da jin dad'i Faruk yace
"Allah Mummy?"
Tace
"Kayi ka gani I promise."
Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon, kusa
da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana doguwar
kujera, sai da ya cire babbar rigarsa sannan ya
zauna yana shafa kan Faruk yace.
"My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai kazo
muci abinci."
Faruk yace
"Ok Daddy."
Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa.
Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah
wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce fara
mai yalwar gashi don kuwa har gaban goshinta ya
fito. Bana tantama ta had'a iri da larabawa. Kamo
hannun mutumin tayi mai suna Adam tace
"Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?"
Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara
fizgarsa sannan yace
"Muje sahibata."
Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka nufi
kan bene inda hannunsu na mak'ale da na juna...

0 comments:

Post a Comment