Friday, May 5, 2017

'Yan biyun da ke manne da juna na son zama Malamai

A kasar Tanzania, 'yan biyun da ke manne da juna - Maria da Consolata Mwakikuti - na shekararsu ta karshe a makarantar sakandare kuma za su kammala karatun sakandaren da zarar sun gama jarrabawa.
'Yan biyun, masu shekara 19, na karatu ne a yankin Udzungwa da ke kudu maso yammacin Tanzania.
Mahaifiyarsu ta mutu bayan ta haife su, mahaifinsu ma ya mutu saboda haka gidauniyar cocin katolika ta Maria Consolata ce ta karbe su ta raine su kuma ta basu sunayensu.
Wakilin BBC, Leonard Mubali ya je ya yi wata ganawa da su.
Ya zauna a ajinsu tare da su a lokacin da suke daukar darasi ya ce kuma suna da kyakkyawar alaka da 'yan ajinsu sannan suna mayar da hankali sosai a darusa.
Ya ce Consolata ta fi surutu da haba-haba da mutane a kan 'yar uwarsa.
Sun shaida wa wakilinmu cewa suna so su zama malaman makaranta kuma suna fata su auri miji daya.
Shugaban makarantar, Edward Fue, ya ce ya kadu a lokacin da ya hadu da matan matasa a shekarar da ta gabata.
Ya ce a lokacin sai ya rasa yadda zai yi ya taimaka musu saboda makarantar ba ta da kayan koyon karatu na musamman.
A yanzu, makaratar tare kuma da taimakon karamar hukuma ta gina musu daki na musamman da za su rika hutawa.
Sun kuma yi hayar direban da zai rika kai su inda suke zama.
Wakilinmu ya ce 'yan biyun da ke manne da juna ba sa so a yi musu tiyata domin a raba su.

0 comments:

Post a Comment