Wednesday, December 7, 2016

Mayakan sa-kai na farautar 'yan IS a Libya

Mayakan sa kai masu biyayya ga gwamnatin hadin kan Libya sun ce suna farautar 'yan gwagwarmayar kungiyar IS da suka rage a cikin birnin Sirte.
Bayan watanni bakwai ana gwabza fada, dakarun Libya sun kutsa gundumar al-Giza al-Bahriya dake kusa da gabar teku, wadda dama ita ce alkarya daya lito da ta rage a hannun 'yan IS.
Wakiliyar BBC ta ce wani kakakin kungiyoyi masu dauke da makaman, ya shaida wa BBC cewa za a ci gaba da ayyukan soji domin kakkabe masu tayar da kayar baya daga birnin, da kuma tabbatar da tsaro a cikinsa. Kuma zai kasance an yi azarbabi a yanzu, idan aka ce an 'yantar da birnin.
Wasu jami'an sojin sun ce wasu daga cikin masu ikirarin jihadin sun sullube daga zoben da aka yi masu, ana kuma fargabar zasu kaddamar da hare-haren tayar da kayar baya daga makwabtan yankuna.
Tun bayan hambarar da gwamnatin marigayi Mu'ammar Ghaddafi, a lokacin juyin-juya-halin da ya afkawa kasashen gabas ta tsakiya, kasar ta Libya ta fada rikita-rikitar siyasa da ta bullowar kungiyoyin 'yan tawaye.

0 comments:

Post a Comment