Tuesday, December 27, 2016

Har da Bature muka kama a dajin Sambisa - Sojin Nigeria

Rundunar sojin Najeriya, ta ce har da farar fata a cikin 'yan Boko Haram din da ta kama, yayin fatattakar 'yan kungiyar daga dajin Sambisa.
A ranar Asabar ne dai shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan kasar albishir cewa an karya lagon Boko Haram.
Kakakin hedikwatar tsaron Najeriyar, Birgediya-Janar Rabe Abubakar, ya shaida wa BBC cewa sun kama 'yan Boko Haram da dama da suka hada da bature a dajin na Sambisa.
Sai dai kuma Rabe Abubakar mai fayyace ko baturen dan wacce kasa ne ba.
Ya kuma ce an yi dauki ba dadi kafin a karbi dajin na Sambisa.
"Mun kama su, mun kakkashe wasu sannan mun shiga wurin da suke ajiye makamansu." In ji Rabe.
Kakakin Hedikwatar tsaron ta Najeriya, ya kara da cewa " yanzu haka sojojinmu ne kawai a dajin Sambisa, babu dan Boko Haram, idan kuma akwai su to sun buya kuma za mu kai gare su."
To amma dangane da batun ko ina Abubakar Shekau ya ke, Rabe ya ce "muna yi ne domin karya Boko Haram ba wai don mutum daya ba. Shekau daya ne daga cikin 'yan kungiyar. Abu mafi a'ala shi ne mun karya Boko Haram."
Sharhi, Usman Minjibir, BBC Hausa
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Najeriya ke ikrarin fatattakar Boko Haram amma kuma daga baya sai labari ya sha banban.
Sau fiye da biyu rundunar sojin Najeriya ke cewa ta kashe ko kuma raunata shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, amma 'yan kwanaki bayan nan sai Shekau din ya yi raddi.
Har wa yau, wasu na ganin ta ya ya za a gama da Boko Haram amma kuma ba a iya ceto ragowar 'yan matan Chibok din ba fiye da 200.
Sai dai kuma masana harkar tsaro na cewa watakila akwai kanshin gaskiya dangane da ikrarin da kasar ta yi cewa ta karya wa Boko Haram din lago, a wannan karon.
Masanan sun dogara ne da irin banbancin hare-haren 'ya'yan kungiyar na yanzu idan aka kwatanta su da na baya musamman a 2014 da kuma farkon 2015.
A baya dai 'yan Boko Haram na iya shiga duk inda suke so, su kuma aiwatar da irin hare-haren da suke son kaiwa.
Amma yanzu za a iya cewa al'amarin ya koma yakin sunkuru ta hanyar kai hare-haren kunar bakin-wake.
Sai dai kuma masharhata kan tsaron sun nemi dakarun Najeriyar da su sake sabon salon yaki domin idan kida ya sauya to ya kamata rawa ma ta sauya.

0 comments:

Post a Comment