Monday, January 18, 2021

AUREN FANSA 3&4

 

AUREN FANSA CHAPTER 3 & 4
Daddare sai da Bilki ta k'ara tada masa da
maganar wasu kud'in inda a ranar sai da ya yi
6ata mata rai fiye da tunaninta sannan ya nuna
mata ta cika son kud'i, duk dai abubuwan da ya
dad'e dasu a ransa shekara da shekaru sai da ya
amayar mata dashi, sum sum ta tashi ta koma
cikin d'aki tsabar borin kunya.
Jingina yayi da kujerar parlon tare da lumshe
idanu don ya samu nutsuwa sai dai bai kai ga yin
hakan ba wayarsa ta fara ruri, kallon screen d'in
wayar yayi yaga sunan da ya bayyana wato My
sister, murmushi ya saki na tsananin farin ciki a
lokaci guda kuma damuwarsa ta 6ace 6at, d'auka
yayi gami da yin sallama, d'ayan 6angaren aka
amsa sannan tace.
"Ya Hamza! Da fatan an wuni lafiya?"
Sai da yayi murmushi sannan yace
"Lafiya lau Amina ya gida?"
"Alhamdulillah, ya Anty Bilki?"
"Tana nan lafiya ya zafi kuma?"
"Lafiya lau ya Hamza, da fatan komai lafiya?"
Yace
"Alhamdulillah ya jiki kuma?"
Ta d'an yi murmushi kad'an sannan tace
"Alhamdulillah gashi nan muna ta fama."
Dariya yayi yace
"To Allah ya raba lafiya."
Tace
"Amin."
Sannan ta kuma cewa
"Ya Hamza akan maganar mu dai ce yasa na kira
ka, kaga yanzu cikina ya shiga watan haihuwa
kuma nasha fad'a maka idan na haifi babyn nan
na baka shi ka rik'a..."
"Amina! Insha Allah ke zaki rik'a babynki sai dai
ki dinga kawo min shi hutu."
Tayi murmushi mai bayyana hak'ora sannan tace
"Ya Hamza na kenan, yaya na na kaina, nidai kayi
min alk'awarin rik'a abinda zan haifa koda bayan
raina ne, shine kad'ai burina a halin yanzu."
Haka kawai sai yaji gabansa ya fad'i cikin firgici
yace
"Kinga Amina, nasha fad'a maki mutuwa lokaci ne
kuma insha Allah zaki ga abinda zaki haifa har ma
ki shayar da shi ki daina fad'in maganganu haka
ba dad'in ji."
Tayi dariya
"Ya Hamza mutuwa fa na kan kowa sanin gaibu
sai Allah nidai alk'awari na zaka rik'e min kaji?"
Nannauyan numfashi ya saki sannan ya d'ora
"Naji shikenan are you happy now?"
"Yeey! Allah ya bar mana kai ya Hamza, nagode!"
Dariya yakeyi sosai itama tana taya sa, sanann ya
kawar da wancan zancen ta hanyar jefo mata
tambaya
"Ya kingama rubuta list d'in abubuwan da kike
buk'ata?"
Tace
"Eh na gama ya Hamza yana hannun Goggo na
bata."
Yace
"Ok zan kar6a insha Allah sai na ga abinda za'a
siya."
Tace
"Toh ya Hamza Allah ya k'ara bud'i."
Sai da suka d'an ta6a fira kad'an sannan sukayi
sallama ko wane yana mai farin cikin ganawa da
d'an uwanshi.
Amina k'anwar Hamza ce uwa d'aya uba d'aya,
bayan nan kuma su kad'ai ne Goggo ta haifa
bayan Amina sai haihuwar ta tsaya, tunda ta haifi
Hamza sai bayan shekara kusan bakwai sannan ta
haifi Amina, kasancewar su biyu ne kacal yasa
suka shak'u da juna sosai Hamza na son Amina
kuma yanaji da ita, kullum suna mak'ale da juna
tun suna yara har kawo yanzu da aure ya rarraba
su kuma, amma kusan kullum sai sunyi waya.
Amina tasha ci ma Bilki mutunci akan halayanta
da take nuna ma Hamza saboda bazata iya jure
ganin d'an uwanta cikin bak'in ciki da k'unci ba.
Mijinta ya rasu tun tana da ciki wata biyar Allah
ya amshi ransa, ga bashi da uwa bashida uba
haka ma shi kad'ai ne mahaifiayarsa ta haifa,
bayan rasuwar tasa ta zauna nan gidanta da ke
cikin garin Katsina a G.R.A.
Wannan kenan!
***
BAYAN 'YAN KWANAKI
Yau weekend ne Hamza baya zuwa aiki don haka
yana gida yana hutawa, bayan ya gama waya da
Amina kamar kullum Bilki ta shigo cikin shirin fita
unguwa ta sha ado sosai tana ta zuba k'amshi. A
hankali yake binta da kallo kafin kuma ya sauke
su kan shigar da tayi. Sanye take da wata silky
doguwar riga mai dogon hannu kalar brown an
mata aikin duwatsu ba laifi rigar ta kamata sai ta
yafa gyalen kayan. Haka ma takalminta mai tsini
ne kalar kayanta da jaka kalar kayan. Har tazo ta
zauna bai bar kallonta ba cike da mamaki, Bilki
tace.
"Hamza zan fita."
Ya kalleta da mamaki yace
"Ina zakije?"
Ta had'e rai
"Gidan Hajiya Laila."
Shima ya had'e rai
"Ba inda zakije."
Ta mik'e zumbur!
"Me kace?"
Yayi banza da ita, ta rik'e k'ugu tana sassarfa
masifa
"Hamza! Gaskiya ka takura min haka kawai! Kuma
ay dah ba haka kake ba wannan k'anwarta taka
duk ta zuge ka."
Tashi yayi a fusace yana nuna ta da yatsa
"Kar ki k'ara saka Amina a cikin zancen mu
saboda babu ruwanta, kina ji na?"
"Ahayye nanaye, an ta6o masa rabin rai, to an
fad'a Amina ce ke zuge ka kayi abinda zakayi."
Bai san lokacin da ya d'auke ta da mari ba yace
"Kisani ni mijinki ne, kuma nafi k'arfin ki
wulak'anta ni, sannan wallahi kika k'ara fad'in
magana makamancin wannan a bakin aurenki!"
Ta zaro idanu waje
"Iyye! Kan mage ya waye, lallai Hamza yanzu kayi
baki, amma tunda ka mare ni don na fad'i gaskiya
shikenan kaje Allah zai saka min."
Yace
"Nidai na fad'a miki ki iya bakinki, kuma fita
bazakiyi ba ay inace dai sai na bada izini ko? To
mugani idan kin isa!"
Har ya tafi ya dawo yace yana mata mugun kallo.
"Magana ta k'arshe ina so ki sani aure zan k'ara
na gaji da zama da mace irinki wadda batasan
inda duniyar ta dosa ba, na aure ki don ina
tsananin sonki amma kisani dole zan k'ara aure."
A fusace ta cakumo masa wuyan riga kamar kura
taga nama.
"Aure Hamza! Baka isa kayi min kishiya ba, ni
kad'ai ce babu k'ari!"
Yayi dariya gami da cire mata hannu daga rik'on
da tayi masa sannan yace
"Kin isa ne ki hana? Ay baki isa ba aure kamar
anyi ne an gama."
Yana gama fad'in haka yayi shigewarsa d'aki ko
kallonta baiyi ba. Yana jin ihuta tana fad'in
"Wallahi babu wacce ta isa ta shigo min gida ta
zauna lafiya, wallahi koma wacece sai na kashe
ta!!!"
Zuciyarsa har wani zafi take masa, kwanciya yayi
kan gadonsa yana mai maida numfashi sama
sama, meyasa Bilki bazata ta6a chanza halayenta
ba? Yasani tun kafin suyi aure yake fama da iri
iren halayenta na nuni da maita akan kud'i, sam
bata gajiya da tambayarsa kud'i, ko lokacin auren
su Goggo taso ta hana don sam tarbiyyar Bilki
bata yi mata ba, batada kamun kai ga shegen
yawo, sai dai a lokacin yadda yake tsananin sonta
baijin zai iya hak'ura da ita, a haka yayi ta lalla6a
Goggo har ta amince akayi auren. Gashi sam bai
iya mata fad'a idan tayi masa laifi sannan bai iya
hanata kud'i idan ta tambayesa ya rasa dalilin da
yasa haka. So da yawa idan ta tambayesa sai yaji
kamar kar ya bata amma sam sai ya kasa haka
yayi ta rayuwa da ita tana cutarsa ba tare da ya
ankara ba. Gashi da anyi abu ta iya kukan k'arya
kuma nan da nan sai zuciyarsa ta karaya yaji yana
tausayinta, a haka ta gano lagonsa abu kad'an
zata sa masa kuka.
Ajiyar zuciya ya saki tare da gyara kwanciya
yanzu yasan mafita d'aya ce ya k'ara aure k'ila
hakan zai sa ya gane banbancin zama da Bilkin,
wata k'ila ma wadda zai aura batada halayen Bilki
ya yarda ya amince zai k'ara auren, tashi yayi da
niyyar shiryawa yaje ya sanar da Goggo ya shirya
ko yau za'a iya d'aura masu aure, wayarsa ta fara
ruri. Goggo ya gani a saman screen d'in wayar
haka kawai gabansa sai da ya fad'i. A sanyaye ya
d'auka gami da yin sallama, da sauri Goggo tace
"Hamza kana ina yanzu?"
Yace
"Ina gida Goggo, lafiya dai ko?"
Tace
"Babu lafiya Hamza, maza maza ka taho asibiti
k'anwarka na nan na nak'uda, kuma ta kafe tak'i
shiga d'akin haihuwar wai sai ka zo, kuma ga
haihuwar tazo kar ta haihu a gaban d'aki Hamza,
kayi sauri don Allah."
A rud'e yace
"Gani nan yanzu wace asibiti ce?"
Tace
"Alheri clinic kayi sauri."
"To." Kawai yace ya fito da gudu daga d'akin,
takalmansa ma daban daban yasa tsabar rud'u ga
gabansa sai fad'uwa yakeyi. Haka dai ya daure ya
figi mota ya fice da sauri, duk da asibitin batada
nisa daga gidansa amma gani yake bazai isa da
sauri ba. Cikin k'ank'anin lokaci Hamza ya iso
Alheri clinic da gudu ya shiga ciki yana tambayar
suna ina. Koda yaje hanashi shiga akayi sai da ya
kira Goggo yace gashi nan sun hana shi shigowa.
Da k'yar ta rok'esu suka barshi ya shigo.
Yana shiga ya iske Amina sai faman nak'uda
takeyi mai zafi tana kiran sunan Hamza tana kuka.
Da sauri ya isa gareta tana ganinsa ta k'ara sautin
kuka tana fad'in
"Ya Hamza na gode da kazo, wata magana zan
fad'a maka."
Jikinsa yayi sanyi yace
"Koma meye ay sai ki bari ki haihu tukunna..."
"Ya Hamza bazaka gane ba bazan iya bari sai na
haihu ba, amma don Allah ka tsaya ka saurareni!"
Ta fad'a cikin muryar tsawa, tashi yayi ya fara
safa da marwa idanunsa sun kad'a sunyi ja, yasan
tatsunniyar gizo bata wuce ta k'ok'i, tabbas yasan
maganar da ta saba fad'a masa yau ma ita d'in ce
zata fad'a masa. Don haka sai yace
"Ko meye zaki fad'a na riga na sani, don haka ki
tashi a shiga dake d'akin kar ki haihu a nan."
Duk'awa tayi tare da fasa wata irin giggitaciyar
k'ara wadda bama Hamza ba har Goggo da
malaman asibitin sai da suka rud'e, fad'i take
"Bazan shiga ciki ba ya Hamza sai kayi min
alk'awari na k'arshe."
Da sauri ya kalleta
"Haba Amina! Meyasa kin faye kafiya ne? Ba mun
gama maganar nan tun tuni ba? Meyasa kike tado
zancen kuma, ki bari ki haihu zamuyi magana."
Girgiza kanta tayi tana hawaye
"Kayya ya Hamza, don Allah kayi min alk'awarin
kawai."
Goggo ce ta sa baki tace
"Hamza kasan zafin haihuwa, kawai kayi mata
alk'awarin a shiga da ita."
Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace
"Na maki alk'awari Amina, Allah ya sauke ki
lafiya."
Duk da zafin nak'udar da Amina keyi ba hanata
yin mumushi ba, sannan tace
"Nagode ya Hamza nagode!"
Juya mata baya yayi don bazai iya jure ganin
Amina cikin wannan halin ba, a haka aka shiga da
Amina rik'e da hannun Goggo wadda aka samu
aka raba su da k'yar."
Goggo kuka takeyi sosai ji take kamar Amina
bazata fito ba idan ta shiga. Hamza ya zo ya
dinga rarrashinta har ya samu tayi shiru.
Minti kusan talatin ana abu d'aya Amina ta kasa
haihuwa, har an fara shawarar ayi mata CS don da
k'yar idan zata iya haihuwa da kanta. Har sun fara
shawarar a sanar da 'yan uwanta Allah cikin
ikonshi ta haihu. Su Hamza suna jin kukan jariri
suka fara murna suna hamdala.
Jim kad'an wata sister ta fito da jariri tana zuwa
su Goggo suka yo kanta, Goggo ce ta fara cewa
"Alhamdulillah! Ta haihu lafiya."
Hamza kuwa hannu yasa ya kar6i babyn yana
kallo kafin kuma ya kalli nurse d'in yana
murmushi sosai. Nurse d'in ce tace
"Ta haifi mace."
"Alhamdulillah!!" Shine kawai abinda suke cewa.
Kafin kuma Goggo tace
"Ina ita Aminar? Ba'a gama kimtsa ta ba mu
shiga?"
Nurse d'in ce tace
"Sai dai kuyi hak'uri..."
"Me kike nufi da kalamanki?" Cewar Hamza a d'an
rud'e, Goggo ma ta rud'e tace
"Bamu gane abinda kike cewa ba."
Nurse d'in tace
"Abinda nake nufi shine kuyi hak'uri Allah ya
amshi kayanshi, ma'ana Amina ta koma ga
mahaliccinmu."
Saura kad'an Hamza ya saki d'iyar sai da nurse
d'in tayi saurin amsar ta, Goggo kuwa in banda
salati ba abinda takeyi kafufuwanta kasa d'aukarta
sukayi ta zauna da sauri.
Hamza zaman k'asa yayi dirshen yana salati kafin
kuma ya fashe da kuka kamar k'aramin yaro.
"Daman Amina tafiya zakiyi da gaske? Tasha fad'a
min mutuwa zatayi na kasa yarda." Haka yayi ta
sambatu kamar zautacce a yayinda Goggo ke
kuka rungume da babyn.
Sai da aka fiddo da gawar Amina lullu6e cikin
farin zanin gado bisa gado mai taya a lokacin
kuma suka gasgata ta mutu d'in. Wurin ya kuma
rud'ewa inda Hamza ya rugo ya rugume gadon
yana magana da gawar Amina. Goggo na tsaye
tana kuka tana tausayin Hamza, da k'yar aka
6am6are shi daga jikin gadon aka sanya ta cikin
doguwar ambulance.
Hamza na tuk'i yana kuka har baya ganin
gabanshi, ga kukan baby dake k'ara rud'a shi.
Can gidan Goggo dake cikin G.R.A suka nufa.
Suna isa aka shiga da gawar a cikin gida.
Bayan anyi ma Amina wanka an mata sutura sai
kuma aka d'auketa za'a kaita makwancinta na
k'arshe, gidanta na gaskiya! Hamza na ji na gani
ya saka Amina cikin kabarinta, Masha Allah Amina
tayi mutane don kuwa har tutse akeyi wurin
sakata a makwancinta.
Bayan an gama kuma suka juyo gida inda su
Hamza suka cigaba da kar6ar gaisuwa.
Itama Bilki kullum sai tazo amma bata ta6a dafo
komai ba a matsayin abincin sadaka ba hasali ma
sai tayi kwalliyarta take zuwa bata nuna wata
damuwa ba.
A haka aka yi sadakar uku ana zaman makoki,
inda Hamza ya dangana yana amsar gaisuwar
kowa saidai fa baya magana sai dai yayi shiru ya
k'ura ma wuri d'aya ido kamar yana tunani. Ko
kuma idan akayi masa gaisuwa sai ya dad'e yana
kallon mutum kafin kuma ya amsa gaisuwar.
Shikenan Amina ta tafi, mutuwa mai yankar
k'auna mai raba tsakani, saidai Allah baya barin
wani don wani yaji dad'i. Allah kasa mu dace,
Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe Amin
thumma Amin.